Biden ya bayyana a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X cewa, "duk da cewa nayi niyar sake yin takara, sai dai ina da yakinin cewar abinda yafi dacewa ga jam'iyyata da ma kasa baki daya shi ne in janye daga takarar tare da mayar da hankali kan kammala ragowar wa'adin mulkina."
Biden ya kara da cewa, nan gaba kadan zai yi wa al'ummar Amurka cikakken jawabi akan lamarin.
Yanzu dai shugaba Biden ya tabbatar da amincewarsa ga mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta maye gurbinsa.
Sai dai an tsara gudanar da babban taron jam'iyyar Democrat na bana, inda a hukumance za'a fidda wanda zai yiwa jam'iyyar takara a tsakanin ranakun 19 zuwa 22 ga watan Agusta mai kamawa a birnin Chicago.
Ku Duba Wannan Ma ‘Yan Democrat Na Bayyana Damuwa Kan Makomar Wasu ‘Yan Takararsu Idan Jam’iyyarsu Ta GazaKu Duba Wannan Ma Yadda Obama Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Takarar Biden
Hakan ya biyo bayan damuwa da wasu ‘yan Democrat suka bayyana game da yadda masu kada kuri’a ke jefa ayar tambaya kan shekarun Biden da kuma damar samun galaba kan Trump a zabe mai zuwa idan ba a yi sauyi ba.