Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Biden Ya Kamu Da Cutar Covid-19


Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Fadar gwamnatin Amurka ta white House ta sanar cewa, Shugaba Joe Biden ya kamu da cutar COVID 19 a ranar Laraban nan, jim kadan bayan ya soke gabatar da jawabi a Las Vegas inda ya shirya zai janyo hankalin al'ummar Latino masu kada kuri’a.

Shugaban mai shekaru 81 a duniya ya kamu da cutar ne kafin taron shi na farko a Las Vegas a ran Laraba, inda ya nuna kananan alamun kamuwa da cutar, a cewar jami’ar hulda da 'yan jarida ta fadar white House, Jean-Pierre cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban ya karbi rigakafin cutar har ma da kari, zai kuma koma gidan shi da ke Rehhoboth, Delaware, inda zai kadaice.

Shugaban Amurka Joe Biden yana tafiya zai shiga jirgi
Shugaban Amurka Joe Biden yana tafiya zai shiga jirgi

Jean tace, Fadar White House za ta rika sanar da halin da shugaban ke ciki, a yayin da yake cigaba da gudanar da daukacin ayyukan ofishin sa a inda ya ke a kadaice.

Ta kara da cewa, "Fadar White House za ta rika bayyana halin da Shugaban kasar yake ciki akai-akai , yayin da yake ci gaba da gudanar da cikakken ayyukansa na ofis lokacin dda yake kadaicen."

Shugaban Amurka Joe Biden zai shiga jirgi zuwa Deleware ya yi jinyar Corona
Shugaban Amurka Joe Biden zai shiga jirgi zuwa Deleware ya yi jinyar Corona

Bayan bayanin na Jean-Pierre, likitan Biden ya ya yi karin bayani cewa, Shugaban kasar yana lunfashi yadda ya kamata an kuma bashi. magani. Likitan, wanda ba a bayyana sunansa ba a cikin sanarwar, ya ce Biden ya nuna alamun da suka hada da mura, da tari da kuma lauyayi.

Yayin da Biden ke shirin hawa jirgin Shugaban kasa "Air Force One" don tashi zuwa Delaware, manema labarai sun tambaye shi yadda yake ji, sai ya daga masu babban yatsa ya amsa cewa, “Lafiya, Ina jin lafiya."

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG