Shugaban Amurka Donald Trump Yana Ziyarar Kasashe Biyar a Yankin Asiya

Shugaba Donald Trump yayinda yake taro da 'yan kasuwar Japan

Shgaban kasar Amurka Donald Trump, yanzu haka yana ziyarar kasashe biyar a yankin Asiya da zummar matsawa Koriya ta Arewa lamba don ta kawo karshen shirin ta na makaman Nukiliya, a jiya Lahadi yayi gargdin cewa “Babu wani mutum, ko mai mulkin kama karya, ko gwamnati… da zata yiwa Amurka kallon raini.”

Trump ya fadawa dakarun Amurka a sansanin Yokota a Japan cewa, “Da hadin gwiwar kawayenmu, jaruman Amurka a shirye suke su kare kasarmu da duk karfin da muke da shi.” ya ci gaba da cewa “a wasu lokuta a baya, suna raina mu, kuma hakan bai kamata ba.

Wani babban jami’i dake cikin tawagar Trump, ya ce yawancin maganganun da yayi Fara Ministan Japan Shinzo Abe da sauran shugabannin da zai gana da su a ziyarar kwanaki 13, zata mayar da hankali ne wajen kawo karshen shirin Koriya ta Arewa na kera makamin Nukiliya.