A halin da ake ciki kuma, nan da nan harin ta’addancin da aka kai a birnin New York ya dau salon siyasa, bayan da Shugaba Donald Trump ya dora laifin kan wani tsarin bayar da visa, wanda ya ce shi ne ya bai wa maharin, Sayfullo Saipov, damar shiga Amurka, sannan Trump ya bayyana tsarin shari’ar Amurka da cewa ‘shirme’ ne, saboda tafiyar hawainiya da tsarin ke yi.
Saipov, wanda ya gaya ma ‘yansanda cewa ya shirya kai harin ne a lokacin shagulgulan Halloween saboda a ganinsa mutane da dama za su fi fitowa da yawa a kan titi, an gabatar da tuhumce-tuhumce kashi biyu a kansa jiya Laraba na aikata manyan laifuka.
Trump ya ce ya na so ya hada kai nan da nan da majalisar dokokin kasa saboda soke irin tsarin visan da Saipov ya yi amfani da shi wajen shigowa Amurka.
Sai dai kuma wadannan kalaman na Trump sun janyo soke-soke daga ‘yan democrat, wadanda suka ce Shugaban kasan na gaggawar maida al’amarin wani abu na siyasa, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke kokarin gano abin da ya faru.