Shugaban Amurka Donald Trump ya sake kare hukumar nan ta “ICE” da aka baiwa aikin tabattarda ana aiki da dokokin kayyade shige-da-fice wacce kuma ‘yan jam’iyyar adawa ta Democrats ke kiran cewa a soke ta.
A cikin daya daga cikin rubuce-rubucen da yayi kan shapinsa na Twitter a karshen makon da aka baro, shugaban ya zargi ‘yan Democrats da cewa suna son a wargaza hukumar ta ICE ne kawai don basa son a rinka tsare kan iyakokin Amurka.
Dubban mutanen Amurka sun wuni jiya suna ta gudanarda manyan tarukkan zanga-zanga a garuruwa da biranen kasar masu yawa, don nuna adawa akan matakin da gwamnatin ta Amurka ke dauka gameda sha’nin shige da ficcen baki, da kuma musamman don neman a hade iyalan da aka raba da juna yayinda suke tsallako kan iyakar Amurka da Mexico.