Shugaban Amurka da Shugaban China Sun Yi Ganawar Bai Daya

Shugaban Amurka Donald Trump ya sha hannu da shugaban China Xi Jinping

A ci gaba da ziyarsa a nahiyar Asiya shugaban Amurka Donald Trump, yau Alhamis, ya yi ganawar bai daya da takwaransa na kasar China Xi Jinping inda ya bukaci shugaban Chinan ya matsawa shugaban Koriya ta Arewa ya watsar da shirin nukiliyarsa

Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban China Xi Jinping, sun yi ganawa ta bai daya da safiyar yau Alhamis, tattaunawar da Trump ya ce zai yi amfani da ita wajen matsa ma Xi lamba, ya sa Koriya Ta Arewa ta yi watsi da shirinta na nukiliya.

Trump ya isa birnin Beijing din ne jiya Laraba, a ziyararsa a matsayin Shugaban kasa a karo na farko zuwa China, babbar aminiyar Koriya Ta Arewa. Ana kyautata zaton Trump zai bukaci China ta kori ‘yan Koriya Ta Arewa da ke kasar ko kuma ta dakatar da wasu daga cikin harkokin da ta ke yi da gwamnatin Koriya Ta Arewar mai Fada a Pyongyang.

Tattaunawar ta Trump da Xi za ta kuma ta’allaka kan batun cinakayya, al’amari mai sarkakkiya ganin yadda Trump ya dade ya na korafin kwarar Amurka da China ke yi a fannin na cinakayya.

Cinakayyar China da Amurka ta karu da kashi 12.2 daga cikin tun daga bara, wadda a fassarar kudi ta kai dala biliyan 26.6, bisa ga kididdigar hukumar Kwastam din China.