Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un, sun yi musayar hannu da kuma gaisawa ta jin dadi da junansu, don kaddamar da taron kolinsu na biyu da ke mayar da hankali akan raba Koriya Ta Arewa da makamanta na nukiliya.
A yammacin yau laraba shuwagabannin biyu suka gaisa a gaban tutocin Amurka da Koriya ta Arewa a hotal din Sofitel Legend Metropole, dake birnin Hanoi, kamar dai yadda suka yi a taronsu na farko da suka yi a watan Yuni bara, a Singapore.
"Abin farin ciki ne dana kasance tare da shugaban Kim," in ji Trump yayin da yake jawabi a gaban manema labarai tare da Kim Jong Un, kafin a ganawarsu ta ido da ido. "Ina ganin taron farko ya sami gagarumar nasara amma ina fatan wannan zai sami irin wannan nasarar ko ma ya zarce hakan."
Shima Shugaba Kim ya nuna gamsuwarsa da wannan ganawar ta biyu da yake yi shugaba Trump, inda har yace,"Na tabbata za a samu nasarar cimma wata muhimmiyar matsaya waccedukan mutanenmu za su yi marhabin da ita."