Trump ya fadawa jaridar Wall Street Journal a jiya Lahadi cewa, akwai mutanen kirki a cikin kwamitin dake zaman shawarwarin daga manyan jam'iyyun kasar biyu. Amma kuma ya bayyana shakkunsa na amince da wani kudi kasa da dala biliyan 5.7 na ginin katanga da yake ta nema a ba shi, Trump ya kara da cewa "dole ne in yi abin da ya dace."
Shugaban ya kuma ce baya tunanin zai amince da baiwa bakin hauren da aka shigo dasu Amurka ta baraubiyar hanya tun suna kanana da ake kira Dreamers damar zama ‘yan kasa ba. Ya ce makomar wadannan bakin hauren da aka shigo da su Amurka tun suna yara wani batu ne na dabam da za a duba a wani lokacin dabam.
Trump ya ce tabbas akwai yiwuwar sake dakatar da wasu ayyukan gwamnati" indai bai samu abin da yake bukata ba domin ginin katanga. Ya kuma ce yana iya ayyana matakin ta baci na kasa wanda zai ba shi damar samun kudin gina katangar ba tare da amincewar 'yan majalisar tarraya ba, matakin da tabbas ‘yan Democrats zasu kalubalanta a kotu.