Shugaban ya ce ba lallai ba ne a yi hakan kamar yadda mujallar Atlantic da ake bugawa a nan ta bayyana a wani rahotonta.
Mujallar ta Atlantic, ta ruwaito wani jami’in fadar White House, wanda ya ji Trump ya na tattaunawa ta wayar tarho tare da shugaban kungiyar ta NRA, Wayne Lapierre, inda ya ke kara jaddada masa matsayarsa, wacce ke nuna cewa, ai dama ana gudanar da bincike gabanin a sayar wa da mutum bindiga, saboda haka ba za a sake waiwayar batun ba.
Bayan hare-haren da aka kai a kwanakin baya a birnin El Paso na jihar Texas da kuma Dayton na jihar Ohio, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama, Shugaba Trump, ya nuna goyon bayan tsaurara bincike a kan duk wanda zai sayi bindiga, amma ga dukkan alamu, ya yi amai ya lashe.
Tun dai bayan hare-haren ne shugabannin masu fafutukar ganin an tsaurara dokokin mallakar bindiga irinsu Joshua Howitz, su ke kiran da a dauki matakan da suka dace
“Ya ce idan har ana so a magance matsalar kai hare-haren bindiga, to ya zama dole a dauki mataki akan mallakar bindiga.”