Shugaba Trump Ya 'Yantar Da Roger Stone

Shugaban Amurka Donald Tump ya yaye wa dadadden mai ba shi shawara Roger Stone zuwa gidan yari ‘yan kwanaki kafin ya fara zaman kaso.

An sami Stone da laifin yi wa kotu karya bayan ya sha rantsuwa kan zai bayyana gaskiya a lokacin da ake binciken yiwuwar katsalandan Rasha a zaben shugaban Amurka na shekarar 2016, aka kuma yanke ma sa hukuncin zama gidan kaso tsawon shekara 3 da wata 4.

“Roger Stone ya riga ya wahala sosai,” abinda wata sanarwar fadar White House ta ce kenan. Ba a yi ma sa adalci ba, da wasu da yawa a wannan shari’ar. Yanzu Roger Stone ya zama ‘yantacce."

Shugaba Trump

Sai dai yaye wa mutum zuwa gidan yari irin wannan ba kamar cikakkiyar afuwa ba ne kuma wannan matakin ba ya wanke laifin da mutum ya yi. Ko da ya ke dai, matakin ya kare Stone daga zuwa gidan yari.

Ranar Talata 14 ga watan Yuli ya kamata Stone ya fara zaman yari a jihar Georgia bayan da wata kotun daukaka kara ta tarayya ta yi watsi da bukatarsa ta neman a kara masa lokaci kafin ya fara zaman kaso.