Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wasu bayanai a shafin sa na twitter jiya Laraba, inda ya sake tado da dadaddiyar takaddamar dake tsakanin sa da hukumomin binciken sirrin kasar, inda yayi watsi da bayannan da suka gabatar game da ‘yan ISIS, da Koriya ta arewa da kuma Iran.
WASHINGTON D.C. —
A wasu rubuce-rubuce da yayi, Trump yayi ikirarin cimma wasu muhimman abubuwa a yayinda ya ce shugabannin hukumar binciken bayanan sirrin suna aiki kamar basu san kansa ba.
Trump ya rubuta cewa, “
a lokacin da na zama shugaban kasa, ISIS ta bazu ko’ina a Syria. An sami gagarumar nasara tun daga lokacin, musamman a cikin makonni 5 da suka wuce.
Nan ba da dadewa ba za a gama da daular ISIS, abinda ba a yi tunanin zai yiwu ba shekaru biyu da suka wuce.
Wadannan rubuce-rubucen na Trump na zuwa ne kwana daya bayan da shugaban hukumar binciken sirrin kasa, tare da shugabannin wasu muhimman hukumomi na binciken sirri, ciki har da CIA, da FBI, da kuma NSA, suka gabatar da jawabin su na shekara-shekara game da barazanar da kasashen duniya ke fuskanta a gaban ‘yan majalisar dokokin Amurka.