Shugaba Trump Ya Sake Barazanar Rufe Kan Iyakar Amurka da Mekziko

  • Ibrahim Garba
Yayin da takaddama kan bakin haure ke dada tsanani a Amurka, Shugaba Donald Trump ya yi barazanar rufe kan iyakar Amurka da Mekziko da kuma katse kudin tallafin da Amurka ke bai wa wasu kasashe don tsai da kwararowar bakin haure.

Shugaban Amurka Donald Trump, jiya Jumma'a ya sake barazanar rufe kan iyakar Amurka da Mekziko (Mexico) kwata-kwata, tare kuma da katse tallafin da Amurka ke baiwa kasashen Honduras da Guetemala da kuma el-Salvador, muddun Majalisar Dokokin Taryyar Amurka ta ki tanadar da kudin gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico.

A wasu jerin sakonnin twitter da ya tura, Trump ya yi kiran da a canza abin da ya kira dokokin shigi da ficin Amurka na shirme, wadanda su ka zama matsala ga Amurka.

Wadannan kalaman na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta shiga rana ta 7 a jere, da wasu sassan gwamnatin tarayya su ka kasance a rufe saboda rigimar kasafin kudi tsakanin Trump, wanda ke son a tanaji dala biliyan 5 don gina katanga, da kuma 'yan Democrat masu goyon bayan samar da kudi kalilan, kuma su ke matukar adawa da batun gina katangar.