Shugaba Trump Ya Jinjinawa Ma'aikatan Amurka

APTOPIX Trump

Sai dai izuwa yanzu babu wani ci gaba da aka samu a kokarin kawo karshen rufe ma’aikatun da ya shiga kwana na talatin da biyu yau.

Trump ya sake jadada kira da a gina katanga kan iyakar Amurka da Mexico a sakonsa na twitter inda yace, “tilas ne muyi aiki tare yanzu, bayan shafe shekaru ana watsi da batun, mu kawo karshen matsalar bukatun jinkai, da masu aikata miyagun laifuka a kan iyakarmu. Zamu yi gagarumar nasara.

A makon nan, Trump ya yi wani tayi da nufin bude ma’aikatun gwanatin inda yace zai bada izini zama Amurka na tsawon shekaru uku ga daruruwan ‘yan gudun hijiran da iyayensu bakin haure suka shigo da su Amurka suna kanana da ake kira DREAMERS, idan zai sami dala miliyan dubu biyar da dari bakwai da yake bukata na gina katanga, da nufin shawo kan matsalar bakin haure.

‘Yan Jam’iyar Democrat dai sun ce akai kasuwa.