Shugaban Amurka Donald Trump ya gayyaci kusoshin ‘yan majalinsun kasa, na bangaren jam’iyyar Republicans da na Democrat, gayyatar da fadar White House ta kira ta “tattaunawa kan tsaron iyakar” kasar.
Wannan tattaunawar za ta gudana ne yayin da aka shiga yini na 12 da rufe wasu ma’aikatun gwamnatin kasar.
Ana dai sa ran shugaban masu rinjaye Mitch McConnel, zai halarci zaman, amma babu tabbacin shugaban marasa rinjaye Chuck Schumer, ko kuma sauran ‘yan jam’iyyar Democrat, da suka hada da wadda ake sa ran za ta zama sabuwar kakakin majalisar Nancy Pelosi, za su amsa wannan goron gayyata.
Sannan babu tabbacin ko bangarorin biyu, za su yi amfani da wannan zama su cimma matsayar da za ta sa a sake bude ma’aikatun gwamnatin.
‘Yan jam’iyyar Democrat za su karbe rinjaye a majalisar wakilai idan Allah ya kai mu gobe Alhamis.
Ana kuma sa ran Pelosi za ta nemi a kada kuri’a kan wasu kudurorin doka biyu, inda kudurin farko, zai ba da dama a samar da kudaden tafiyar da ma’aikatun da aka rufe har zuwa karshen watan Satumba.
Sannan na biyun, zai ba da damar a samar da kudade ga ma’aikatar tsaron cikin gida ta Homeland Security, wacce za ta yi amfani da su har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu.
Sai dai kudurin dokar, ba ya dauke da bukatar da Trump ya gabatarwa majalisar ta samar da dala biliyan $5 domin gina Katanga.