Shugaba Trump Ya Fara Juyawa Rasha Baya Akan Ukraine

Shuwagabannin kasashen duniya masu karfin tattalin arzikin kasa na kungiyar G20 sun hallara a kasar Argentina domin gudanar da taron shekara shekara na bana 2018.

Yau Juma’a shugaban Amurka Donald Trump, ya fara wani taron kwana biyu da shuwagabannin duniya a babban birnin kasar Argentina.

Shugabanin sun hallara domin gudanar da taron kasashen duniya da suka fi karfin tattalin arziki na G20. Sai dai wani takwaran aikinsa da shugaba Trump ba zai gana da shi ba, shi ne Vladimir Putin na Rasha.

Shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, tun da Rasha ba ta saki jiragen ruwan Ukraine da matukansu ba, ya fi kyau dukkansu su soke wannan zama da aka shirya za a yi.

A baya, an tsara wani zama tsakanin Trump da Putin a gefen taron na G20 har na tsawon sa’o’i biyu, duk da sukar da wasu Amurkawa ke yi da kawayenta na NATO, dangane da kwace jiragen ruwan Ukraine da Rashan ta yi, hade da matukanta a ranar Lahadi.