Shugaban Amurka Donald Trump ya dage a kan cewa takardar nan da ake cacar baki akan ta, dake zargin hukumar FBI a binciken katsalandar da Rasha tayi a zaben shekarar 2016 da wuce gona da iri, cewa takardar ta wanke shi kwata kwata, amma kuma daya daga cikin wadanda suka rubuata takardar ya musunta tunanin na Trump a jiya Lahadi.
Dan majalisar wakilai dan Republican Trey Gowdy daga jihar Carolina ta Kudu, daya daga cikin wadanda suka taka rawar gani wurin fid da takardar da kwamitin tattara bayanan sirri na majalisar ya shirya, ya fadawa shirin gidan telbijin na CBS mai suna Face the Nation a jiya Lahadi cewa, wannan takardar ba ta shafi aikin wata guda da kwamitin Robert Muller yayi a kan binciken hadin bakin yakin neman zaben Trump da Rasha ko kuma Trump din na yin katsalanda ga binciken ba.