Shugaban Amurka Donald Trump ya fada jiya Alhamis cewa shi bai san da zaman shafin yanar gizon WikiLeaks ba, bayan da aka kama wanda ya bude shafin na kwarmata bayanai wato Julian Assange a Burtaniyya.
Mutumin dan shekaru 47 da haihuwa, dan kasar Australia dama a ofishin jakadancin Ecuador dake birnin London yake boye tun daga shekarar 2012, amma aka bankado shi aka kuma tusa keyar sa jiya Alhamis, yanzu haka yana hannu ‘yan sandan Burtaniyya.
Kasar Ecuador ta ce Assange ya saba ka’idodin neman mafaka saboda ya ci gaba da yin katsalanda a harkokin wasu kasashe ta hanyar wallafa wasu muhimman bayanan sirri.
A jiya Alhamis ne ‘yan jarida suka yi wa shugaba Trump tambayoyi akan kamen na Assange, inda kuma yace shi bai san komai ba gameda wannan shafin na WikiLeaks, har ya kara da cewa “wannan ba irin abinda na ke da lokacin sa bane.”