Shugaban Amurka Donald Trump ya ce mai yiwuwa ganawar da aka shirya yi tsakaninsa da Shugaban Koriya Ta Arewa a watan gobe, ba za ta tabbata ba.
“Idan ba a yi ba, watakila za a yi nan gaba,” a cewar Trump. Ya kara da cewa, “Mai yiwuwa ba za a iya yi a ranar 12 ga watan Yuni ba.”
Da ya ke magana a fadarsa da Shugaban, Koriya ta Kudu Moon Jae-in, Trump ya ce, “Akwai wasu yanayi da mu ke son gani. Ina jin za mu samu wadannan yanayin.”
Da aka tambaye shi irin yanayin da yake nufi, sai Trump ya ce, “Bai kamata na fada ba.” To amma batun kawar da makamin nukiliya a Koriya ta Arewa “Dole ya faru.”
Shi ma da ya ke bayani a taron manema labarai da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kira, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce har yanzu Amurka na shirye-shiryen ganawar a ranar 12 ga watan Yuni, to amma bai tabbatar ko ganawar za ta yiwu ba. To amma ya ce ya na da karfin gwuiwar cewa karshenta dai za a kai ga ganawar.