Shugaba Trump Na Sa Ran Za a Samu Riga-kafin COVID-19 Nan Da Karshen Shekara

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana da kwarin gwiwar cewa nan da karshen shekarar nan, za a samar da riga-kafin cutar ta COVID-19 wacce za a yi wa jama’a cikin hanzari.
Trump wanda bai ba da cikakkun bayanai, ya kara da cewa, “ba da bata lokaci ba kuma za a rarraba allurar riga-kafin, domin har an sa dakarun kasar cikin shirin kar-ta-kwana.”
Sai dai hasashen shugaban na Amurka ya yi hannun riga da shaidar da Majalisar Dokokin kasar ta saurara gabanin Trump din ya yi wannan jawabi daga Fadar gwamnatin Amurka ta White House a jiya Alhamis.
Domin korarren Daraketan hukumar samar da alluran riga-kafi a Amurka, Dr. Rick Bright, ya fadawa ‘yan majalisa cewa, “babu wani shiri da aka yi wajen samarwa da kuma raba allurar riga-kafin cutar, yana mai cewa hakan zai iya faruwa ne cikin wata 12 ko 18 masu zuwa – idan komai ya tafi daidai.
A halin da aka ciki, sama da alluran riga-kafi 90 ne ake kan gwadawa a sassan duniya, inda wani kamfanin hada magunguna a kasar Jamus da ake kira CureVac a jiya Alhamis ya ce, daya daga cikin allurar riga-kafin da yake gwadawa ya kare dabbobi daga kamuwa da cutar ta corina. Ana kuma sa ran a wata mai zuwa za a fara gwajinta akan bil adama.