Shugaba Trump Da Takwaran Aikinsa Na Kasar China, Xi Jinping Sun Gana Akan Koriya Ta arewa

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yace, “babu wata jayayya akan Koriya ta Arewa” tsakanin Amurka da China bayan tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na kasar China, Xi Jinping.

Tillerson wanda yake Beijing, babban birnin kasar China tare da Trump, ya gana da manema labarai yau bayan tattaunawar shugabannin biyu da ta maida hankali akan Koriya ta Arewa da kuma harkokin cinikayya. Yace shugabannin biyu sun fito fili sun gayawa juna gaskiya kan batun kare hakin bil’adama, da rikicin da ya shafi tekun kudancin China.

Dangane da Pyongyang kuma, yace kasar China ta bayyana karara a tattaunawar ta kwanaki biyu cewa, ba zata amince Koriya ta arewa ta mallaki makaman nukiliya ba.

Tun farko Trump ya bayyana cewa, tilas ne Amurka da China su hada hannu wajen ceto yankin da duniya baki daya daga abinda ya kira gagarumar barazanar da gwamnatin Koriya ta arewa ke yi.

maimaita kurakuran da aka yi a baya ba dangane da Pyongyang, wadda a cikin shekarun nan ta habbaka ayyukanta na nukiya.