Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi korafi kan manyan laifukan da aka ce an samu tsohon manajan gangamin yakin neman zabensa, Paul Manafort da su, wadanda ka iya sa ya fuskanci hukuncin zaman gidan yari na tsawon gwamman shekaru.
A jiya Talata, shugaba Trump ya fadawa manema labarai a filin tashin jirage na Yeager da ke Charleston a jihar West Virginia cewa, “wannan wani abin bakin ciki ne da ya faru” yana mai cewa bai ji dadin wannan abu da ya faru da Manafort ba, wanda aka samu da laifuka takwas na almundahana da aka tuhume shi da su.
A wani lamari mai kama da wannan, wanda ake ganin babban koma-baya ne ga shugaba Trump, wanda kuma ya faru a daidai wannan lokaci da aka samu Manafort da laifi, tsohon lauyan Trump da suka dade suna aiki tare, Michael Cohen, ya amsa laifin tuhume-tuhumen da ake masa, inda har ya bayyana cewa, an biya wasu mata biyu kudaden toshiyar baki, “da nufin matakin zai yi tasiri akan zaben” Amurka, wanda dan takarar shugaban kasar a shekarar ta 2016 ya ba da umurnin a yi, watau shugaba Trump.