Suna ihu suna cewa, "babu kiyayya, babu razanarwa, muna maraba da 'yan gudun hijira anan," masu zanga zanga suna auna dokar da shugaba Trump ya bayar, wacce ta tsaida zuwan 'yan gudun hijira Amurka na wata hudu. Haka nan dokar ta hana wadanda suka sami visa daga kasashen Iran, da Libya, da Somalia da Iraqi, da Sudan da Yemen shiga Amurka na tsawon kwanaki 90. Dokar ta kuma dakatar da zuwan 'yan gudun hijira daga Syria har sai illama sha'allah.
Wani ba-Amurke dan asalin kasar Somaliya, wanda yake zaune nan shekaru 10 da suka wuce, ya fadawa Muryar Amurka cewa, an hana matarsa dawowa jiya Asabar, lokacinda ta sauka a tashar jiragen sama na Dulles dake Virginia. Kodashike an kyale 'ya’yanta su zauna, amma ita bata yi dace ba.
Jiya lahadi shugaban na Amurka bai damu ba sam da ci gaba da samun masu adawa da dokar da ya bayar. Yace "kasarmu tana bukatar kan iyakoki masu karfi, da kuma bincike mai tsanani yanzu. Dubi abunda yake faruwa a duk fadin turai, da ma fadin duniya baki daya. Kamar yadda ya fada ta shafinsa na Twitter ga masu mu’amala da shi su kusan milyan 23.