Shugaba Tinubu Ya Yi Ta'aziyar Rasuwar Tsohon Ma'aikacin Muryar Amurka Kabiru Fagge

  • VOA

Kabiru Fagge and President Bola Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana alhininsa game da rasuwar babban ma’aikacin yada labarai, Kabiru Usman Fagge, wanda ya rasu ranar Juma’a a kasar Amurka.

Fagge, mai shekaru 77, ya kasance shahararren dan jariya da ya yi fice a duniyar Hausa domin dadewa yana aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), wanda ya shafe shekaru 25 yana aikin.

A cikin sakon ta’aziyya, shugaba Tinubu ya yaba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen gina kasa, musamman wayar da kan jama’a da bayar da shawarwarin ilimi ta hanyar fitaccen shirinsa na ilimi na mako-mako da ya kwashe shekaru yana yi.

"Burinsa na yiwa bil'adama hidima ta aikin jarida ya fara tun da wuri, tun daga lokacin da yake aikin a matsayin mai zaman kansa a lokacin da yake koyarwa. Muna godiya da ayyukan da ya yi ta hanyar da ya zaba da kuma kasancewarsa jakadan Najeriya nagari a irin wannan dandalin na duniya," in ji shugaban.

Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan marigayin, gwamnati, da al’ummar jihar Kano, da kuma ‘yan jaridun Najeriya bisa wannan rashi.