A yau Alhamis, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karbi bakuncin Shugaban Senegal a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja, birnin tarayyar Najeriya.
Kafaffen yada labaran cikin kasar Najeriya sun ruwaito cewa Shugaban na Sengal ya zo ziyarar aiki a Najeriya ne.
Saidai ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu masaniya akan aikin da ya kawo Shugaban Senegal din Najeriya.
A watan Afrilu da ya gabata ne aka rantsar Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal bayan ya ni nasara da kashi 54 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam'iyyu masu mulki.
Kuma Shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ya bi sahun sauran shugabannin kasashen yankin domin halartar bikin a cibiyar Diamniadio Exhibition Centre.
Ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar da wasu manyan jami'an gwamnati ne zasu raka shi a wannan ziyarar.