A yanzu haka dai ana sayar da kudin kasar tsakanin GH₵14.50 zuwa GH₵15 a dala daya, ‘yan kasuwa sun nuna cewa suna dora kudaden da ake karawa kan ‘yan kasa masu sayen kaya, wanda hakan ya haifar da tashin gwauron zabi na kayayyaki da na ayyuka.
Faduwar da sidin Ghana ke yi ta haifar da babbar damuwa a tsakanin 'yan kasuwa a duk fadin kasar, wadanda suke bayyana irin illar da lamarin ke yi ga kasuwancinsu.
Da yawa daga cikin ‘yan kasuwa na kara shiga cikin damuwa, inda wasu ke fama da tarin basussuka.
Kungiyar Abinci da Abin sha ta Ghana (FBAG) ta yi karin haske kan yadda tsarin kasuwancin na sayar da kayayyaki a kan bashi ya kara ta’azzara matsalar, yayin da masu shigo da kaya ke kokarin biyan basussukan da ake bin su.
A wani taron manema labarai, Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar, Dr. Cassiel Ato Forson ya dora laifi a kan mataimakin shugaban kasa kuma ga kujeran kwamitin kula da tattalin arzikin kasa game da abin da yake kallo a matsayin gaza magance faduwar darajar kudin kasar.
Dr. Ato Forson ya jaddada mummunan tasirin da faduwar sidi ke yi ga kasuwanci, inda ya nanata kira ga daukar matakan gaggawa wurin shawo kan wannan matsala.
Dandalin Mu Tattauna