A ranar Litinin din da ta gabata, Amurka da Korea ta Kudu suka fara atisayen, wanda ake shirin kammala shi a ranar 20 ga watan nan na Agusta.
WASHINGTON D.C. —
Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce, takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, Kim Jong Un, ya “dan ba da hakuri” saboda gwajin makamai masu linzami da kasarsa ta yi.
Ya kuma kara da cewa, Shugaba Kim, ya sha alwashin, zai dakatar da gwaje-gwajen, da zaran Amurka da Korea ta Kudu ,sun kammala atisayen hadin gwiwar da suke yi.
Shugaban na Amurka ya ce, Kim ya ba da hakurin ne, a wata wasika da ya aiko masa, ya kuma ce, yana da burin “su hadu su tattauna” bayan an kammala atisayen.
A ranar Litinin din da ta gabata, Amurka da Korea ta Kudu suka fara atisayen, wanda ake shirin kammala shi a ranar 20 ga watan nan na Agusta.