Shugaba Jonathan Ya Kasa Gabatar Da Kasafin Kudin Badi

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Kowace shekara a dai dai wannan lokacin shugaban kasar Najeriya ya kan bayyana gaban majalisun kasar ya gabatar da kasasfin kudin shekara mai zuwa to amma ba haka abun yake ba wannan lokacin.
Duk da tsauraran matakai da jami'an tsaro suka dauka da shirin da 'yan majalisu suka yi tun daga karfe bakwai zuwa goma sha daya na safe domin karban babban bako, shugaba Jonathan bai bayyana gaban 'yan majalisun ba.

Dama ana jiran shugaban ne ya bayyana gaban 'yan majalisun domin ya gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa. Sai dai hakan bai samu ba. A hangen 'yan majalisun lamarin ba zai rasa nasaba da rashin daidaito kan farashin gangan danyan mai ba. Tun da jimawa 'yan majalisun da shugaban basu cimma matsaya daya ba kan farashen.

Dan majalisar dattawa Kabiru Marafan Gusau ya ce kodayake shi bai ji wani abu ba amma rashin jituwa tsakanin majalisar dattawa da na wakilai da fadar shugaban kasa kan farashe daya shi ne dalili. Ya ce dole ne bakinsu ya zo daya kafin a ce an yi batun kasafin kudi. In ji sanato Gusau an yi harsashen cewa cikin makon da ya wuce za'a iya cimma matsayi daya shi ya sa aka shirya ya zo, to amma hakan bai samu ba. Yanzu dole wani kwamitin hadin gwiwa ya zauna ya warware lamarin.

Sai dai 'yan majalisar wakilai suna da ra'ayi daban. Sun ce su basu ji dadin rashin zuwan shugaban kasar ba. Dan majalisar wakilai Ibrahim Bello Rigachukunya ce yakamata shugaban ya zo ya bayyana kasafin kudin domin su san abun da zasu fadawa wadanda suka turosu zuwa majalisa domin kada jama'a su dauka ana wani rufa-rufa ne da su. Dangane da kasafin kudin wannan shekarar ya ce su basu gamsu da aikin da gwamnatin ta yi ba. A nasu ganin aikin da aka yi bai kai kashi 75 cikin dari na kasafin kudin kamar yadda ministar kudi ta yi ikirari. Ya ce su basu ga abun da ya wuce kashi 20 ba. Sabili da haka su ba zasu yi shiru ba kada jama'a su ce ana muna-muna da 'yan majalisa. Ba'a gyara aikin shekarar 2013 gashi kuma ana batun shekarar 2014. Idan basu dage a yi gaskiya ba jama'a ba zasu gane abun da suke yi ba. Dole ne su kare mutuncin jama'a da suka turosu nan da kuma nasu mutuncin.Ya ce shugaban kasa dole ya zo ya yi masu bayyani domin wadanda suke wakilta.

Sanato Alkali Jajere ya ce rashin cimma daidaituwa kan farashin gangan mai bai hana shugaban kasa gabatar da kasafin kudi ba.Ya ce shi kasafin kudin menene anfaninsa ga jama'ar kasar domin tun lokacin da ya shiga majalisar ba'a taba aiwatar da kasafin kudi kamar yadda suka amince a yi ba. Ya ce sai a tsaya ana kwarya-kwarya kana su ma'aikatan gwamnati su tsaya suna shata karya. Ya ce bara aikin kashi 43 aka yi. Haka kuma bana bayan sun zaga kasar kashi 42 ne kawai bayan duk kudaden sun shigo aljihun gwamnati. Ya ce sai a tambaya ina ne gizo ke saka. Ya ce shi ne dalilin da ya sa majalisun dokoki da na zartaswa su kan yi hannun riga da juna abun da bai kamata hakan ya faru ba.

Madina Dauda nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Jonathan Ya Kasa Bayyana Kasafin Kudin Badi - 4:40