Shugaba Jonathan Ya Bude Aikin Tashar Samar da Wutar Lantarki

Tashar samar da wutar lantarkin dake Jihar Neja, zata iya samar da Megawatt 700 na wutar lantarki idan an kammala aikin gina ta
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, ya kaddamar da aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta Zungeru dake Jihar Neja a yankin tsakiyar Najeriya.

Shugaban ya ce a bayan samar da wutar lantarki da karfinta zai iya kaiwa Megawatt 700, madatsar ruwan da za a gina zata kuma samar da ruwa ga gonaki masu yawan gaske domin gudanar da ayyukan noman rani a wannan yanki.

An yi kiyasin cewa za a kashe kudi sama da naira miliyan dubu 162 wajen gina wannan tashar wutar lantarki.

Gwamna Babangida Aliyu na Jihar Neja, da manyan sarakuna da jami'an gwamnati suka tarbi shugaba Jonathan a wurin bukin da aka gudanar na kaddamar da wannan aikin, daga inda wakilin sashen Hausa, Mustapha Nasiru Batsari ya aiko da wannan rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Goodluck Jonathan Ya Bude Aikin Tashar Wutar Lantarki Ta Zungeru - 1:50