Shugaba Donald Trump Zai Sha Rantsuwar Kama Aiki A Wa'adi Na 2

Mounted police ride past a security fence in Washington, DC, on January 18, 2025, as the US capital prepares for the inauguration of US President-elect Donald Trump January 20. (Photo by ANDREW CABALLERO-REYNOLDS / AFP)

Akalla mutane 600 ne ake sa ran za su halarci bikin da aka mayar Cikin Majalisar Dokokin Amurka saboda matsanancin sanyi sabanin yadda aka saba bukin a farfajiyar Majalisar dokokin Amurka.

Wata daddaiyar ala'dar da aka fara kunsan shekaro 250 da suka gabata a Demokradiyyar Amurka shine bukin mika mulki cikin lumana bayan shekaru hudu (4), wanda zai gudana a yau Litinin, inda za a rantsar da Donald Trump, shugaban Amurka na 45 wanda ya fadi zaben neman tazarce a wa'adi na biyu a zaben 2020, a matsayin shugaban Amurka na 47 bayan nasarar da ya samu a zaben Nuwamban bara.

miliyoyin Amurkawa ne ake sa ran zasu kali bukin da za a yada ta talabijin yayin da Donald Trump mai shekaru 78 zai sha rantsuwar kama aiki na wa'adin shekaru hudu a fadar White House, yayin da shugaba Joe Biden zai yi salama da fadar White House bayan wa'adin mulki daya kawai.

Sai dai kuma, kimanin mutane 600 ne zasu kalli bukin rantsar da Trump din kai tsaye, inda Trump ya bukaci a mai da bukin cikin Majalisar dokokin Amurka a Capitol Rotunda.

Wani yanayin sanyi da aka fuskanta da daren jiya Lahadi wanda ya kado iska mai sanyi daga kuryar duniya ya ratsa Washington, ka iya sa a fudskanci matsanancin sanyin da ya kai kasa da maki 6 a ma'aunin celcius, da tsakar ranar yau Litinin, dai dai lokacin da bisa al'ada ake gudanar da bunkin rantsarwar a dakalin farfajiyar majalisar dokokin Amurka dake daura da National Mall.

Ana kyautata zaton wannan bikin rantsar da shugaban kasar da za ayi ya kasancewa wanda a kayi cikin matsanancin sanyi a Washington, tun bayan shekaru 40 da suka gabata, lokacin da aka rantsar da shugaba Ronald Reagan, a wa'adin shugabancin shi na biyu, wanda shima aka mai da bukin cikin majalisar a 1985.

Haka zalika kuma an soke faretin da aka saba kaddamarwa daga majalisa zuwa fadar White House ta kan titin Pennsylvania avenue saboda matsanancin yanayin sanyin.