Trump Ya Ce Bashi Da Niyar Sake Rufe Ma'aikatun Gwamnati

Bayan gwagwarmayar da aka kwashe wata daya anayi tsakanin yan Majalissar Dokokin Amurka da shugaba Donald Trump, akan samar da kudin da zai gida katanga tsakanin iyakar Amurka da Mexico, wanda ya janjo aka rufe wasu ma'aikatun gwamnatin Amurka.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce Shugaba Donald Trump na yunkurin kauce wa sake rufe maikatun gwamnatin tarayya amma kuma har yanzu dai ya na da niyar gina katanga tsakanin iyakar Amurka da Mexico, matakin da har yanzu ‘yan jam’iyyar Democrats ke adawa da shi.

“Shugaban ba ya so a sake rufe maikatun gwamnati- ba shi ne burin ba”, a cewar Sakatariyar yada labarai ta Fadar White House Sarah Sanders jiya Litinin, yayin da take ganawa da manema labarai, inda kuma ta nemi ‘yan Democrats su maida hankali akan batun gyara harkan tsaro, a ciki, har da ba da kudin gina katanga.

An bude ma'aikatun gwamnatin tarayya bayan rufe war da aka yi na lokaci mafi tsawo a tarihin Amurka. A karshen satin da ya gabata ne Trump ya sa hannu a kan wani kasafin kudi na wuccin gadin da ya bada damar a sake bude ma’aikatun na tsawon mako uku.