Shugaba Donald Trump Ya Marabci Firayin Ministan Iraqi Da Tawagar Sa

Shugaban Amurka Donald Trump, yayi marhabin lale da Firayin Ministan Iraqi da tawagar sa a fadar White House a jiya littini. Dalilin wannan ziyarar ko ita ce yadda kasashen biyu zasu hada hannu da juna domin su yaki ‘yan kungiyasr IS dake arewacin kasar ta Iraqi.

Lokacin da aka fara tattaunawar Shugaba Trump, ya yaba wa gwamnatin ta kasar Iraqi kan kokarin da take yi domin fuskantar masu tsattasuran raayin addini.

kana ya fadawa Firayin Minister Haider Al-Abadi, cewa yana fata su cimma matsaya akan ratar da aka samu wanda kungiyar IS, ta samar lokacin da ta kwace ikon wurare mafi yawa a arewaci, da kudancin Iraqi a shekarar 2014.

Trump, yace wajibi ne mu samar da wata hanya kwakkwara, domin babban abinda zamu sa gaba shine ganin mun fatattaki kungiyar IS.

Shugaban na Amurka ya bayyana damuwar sa na yadda Amurka, ta janye sojojinta a Mosul, da wasu sassan Iraqi, cikin shekarar 2011.

Yace shawarar da aka yanke tun a shekarar 2008, kuma gwamnatin shugaba Obama, ta aiwatar bayan an cimma yarjejeniya tsakanin Iraqi, da Amurka, amma kuma ta janye bayan an gaza cimma matsaya akan kariya ta musammam ga sojojin Amnurka, da masu aikin kwantiraqi.

Shugaba Trump, yace bai kamata ace mun fita daga wannan yarjejeniyar ba, idan haka ne to tun farko dama bamu yadda an kulla yarjejeniyar ba.