Shugaba Donald Trump Ya Fara Tuntubar Gaggawa Kan Koriya Ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara wata tuntububar diplomasiya ta gaggawa da Japan da Koriya ta Kudu dangane da batun gwajin makamai masu linzami da Koriya ta Arewa tayi da zasu kai wadansu kasashen duniya.

Trump ya yi Magana ta wayar tarho da PM kasar Japan Shinzo Abe na kusan sa’a guda da safiyar yau Litinin agogon Tokyo.

Wata sanarwar fadar White House tace Trump da Abe sun amince cewa, Koriya ta Arewa tana barazana kai tsaye ga Amurka da Japan da Koriya ta Kudu da kuma sauran kasashe, kuma kasashen biyu sun kuduri aniyar kara matsin lambar diplonasiya da kuma a fannin tattalin arziki.

Abe ya shaidawa manema labarai cewa, shi da shugaban kasar Amurka sun amince da cewa, “tilas mu dauki Karin matakai”.

Shugaba Trump ya kuma yi kokarin tuntubar shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in, wanda ke hutu a halin yanzu, bisa ga cewar jami’an Amurka.