Shugaban Amurka Donald Trump ya dawo birnin Washignton bayan da ya yi hutun ThanksGiving a wurin shakatawarsa na Palm Beach da ke jahar Florida, a gabanin kokarin da ‘yan Majalisar Dattawan Amurka ke yi na kada kuri’a kan garanbawul din dokar haraji a wannan makon.
Ana kyautata zaton Shugaban kasar zai halarci liyafar cin abincin da ‘yan Majalisar Dattawa na Republican na mako-mako, wanda za a yi gobe Talata, inda za a tattauna kan wasu muhimman batutuwa na manufofin jam’iyyar Republican.
Wannan ne karo na biyu cikin ‘yan makonnin da suka gabata da Shugaba Trump zai tafi ginin Majalisar Dokokin kasar don zawarcin ‘yan' uwansa ‘yan Republican su goyi bayan garanbawul din da aka yima tsarin haraji.
Tunda farko a wannan watan, Majalisar Wakilai ta kada kuri’ar amincewa da wannan mashahurin garanbawul mafi girma cikin shekaru 10. An tanaji rage haraji ga rukunin jama’a bisa ga yanayinsu na tsawon shekaru, a yayinda kuma aka yi ragi na dindindin ga kamfanoni, wanda hakan zai kara bashin da ake bin Amurka da dala tiriliyan 1.5 cikin sama da shekaru 10.