Shugaba Donald Trump ya ci gaba da kyamfe a shafinsa na Twitter jiya jumma’a, yana caccakar binciken da ake gudanarwa game da yiwuwar hadin baki a tsakanin kwamitin yakin neman zabensa da kasar Rasha.
Trump ya rubuta a jiya cewa, “Mutumin da yace na kori darektan hukumar FBI, yanzu kuma yana bincike na game da korar darektan hukumar FBI. Bita da kulli kawai.”
Wannan caccaka ta baya bayan na da Trump yayi a shafinsa na Twitter tana zuwa ne a bayan da jaridar Washington Post ta bada labarin cewa mai bincike na musamman, Robert Mueller, yana bin sawun hada-hadar kudi ta surukin Trump, Jared Kushner, wanda babban mai bayar da shawara ne ga shugaban, mahaifin matarsa.
Binciken da Mueller ke gudanarwa ya kuma hada da gano ko shugaba Trump yayi kokarin yin kafar ungulu ga shari’a wajen wannan binciken.