Wata kotu a kasar Indiya ta sami wasu mutane shida da laifi a wani harin bam da aka kai a shekarar 1993, a wani wajen hada-hadar kudade dake birnin Mumbai, wanda kuma ya kashe mutane 257.
Kotun ta sami mutane shidan da laifuka da suka hada da kisa da safarar makamai da kuma shirya kai harin ta’addanci. Lauya mai gabatar da ‘kara ya ce da alamu mutanen zasu iya fuskantar hukuncin kisa idan kotu ta yanke hukunci mako mai zuwa.
An dai kame mutanen ne tun wasu shekaru masu yawa bayan da aka kai harin, inda wasu bama bamai masu karfin gaske guda 13 da aka ajiyesu cikin mota suka fashe a wajen hada-hadar canji na Mumbai, da kuma wani babban otel da ke kusa da gurin.
Baya ga mutanen da suka rasa rayukansu, sama da mutane 700 sun raunata a dalilin harin da ya kwashi sa’o’i biyu.
Biyu daga cikin mutanen da aka samu da aikata laifin, ana kyautata tsammanin sune suka shirya harin.
Facebook Forum