A cikin wasikar da shugaba Buhari ya rubutawa majalisar dattawa wadda kakain majalisar Sanata Bukola Saraki ya karanta, ya nemi majalisar da ta bashi karfe goma na safiyar Talata mai zuwa ya gabatar masu da kasafin kudin shekara mai zuwa.
Kasafin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta dauki dumi da yawan korafe-korafe na rashin kudi, wani abu da shugaban kula da kwamitin dake nazari akan kasafin kudi na majalisar wakilai Timothy Ngwelu yace akwai bukatar yin wata doka da zata kafa wata cibiya ta musamman da zata shiga tsakanin majalisa da bangaren zartaswa wajen shirya kasafin kudi.
Yace bayan kundun tsarin mulkin kasa dokar kasafin kudi ita ce ta biyu a duk fadin duniya. Idan ba'a yi kasafin kudi daidai ba to ba za'a samu ganewa ba akan yadda za'a yi aikin gwamnati..Rashin fahimta na kawo rudani tsakanin bangaren zartaswa da majalisa.
Idan akwai fahimtar dokar 'yan majalisun zasu amince da ita domin bangaren zartaswa nada tashi. Kazalika shi ma shugaban kasa zai yi na'am da dokar domin zata taimakeshi a aikinsa..
Kasafin kudin da Shugaba Buhari zai gabatar wani sabon ne da ba'a taba anfani dashi ba a kasar, wato zero based budget.
Kasafin kudin nera tiriliyon shida ne da 'yan kadan kuma an ginashi ne akan farashin gangar mai dala 38 a kasuwar duniya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5