Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada amincewarsa kan nada Malam Lawal Musa Daura a matsayin sabon babban daraktan hukumar tsaron cikin gida ko SSS a takaice.
Malam Lawal Musa Daura ya maye gurbin Mr. Ita Ekpeyong wanda shi ma aka sauke nan take. Wannan canjin ya zo ne a daidai lokacin da 'yan kasar suke nuna bukatar dake akwai na daukan matakan yin garambawul ga hukumar saboda kaurin sunan da tayi a idon wasu 'yan Najeriya dake ganin ana yin kama karya wajen gudanar da ita.
Wani mai fashin baki akan sha'anin tsaro a Najeriya Janar Abdulrazak Umar yayi tsokaci akan nadin. Yace idan ka shiga gida ka tarar da mai tsaro wajibi ne ka samo wanda ka yadda dashi. Saboda haka amincewa da nadin Lawal Daura ba sai an yi wata tantama akai ba.
Dangane da gyare-gyaren da ya kamata Malam Lawal Musa Daura ya yi Janar yace abu ne mai sauki domin kowace hukuma tana da nata tsare-tsaren. Kowace hukuma bata ingantuwa sai ta bi ka'idojinta. Ka'idojin SSS za'a bi yanzu.
Misali, yakin da ake yi da Boko Haram su 'yan SSS ya kamata su dinga gudanar da bincike tun daga kasa-kasa har su gano tushen abun. Bayan hakan sai a fita da shirin yakarsu ba wai a kama wannan a taba ba gobe a bari a yi wani ba.
Ga karin bayani a rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5