A yayin da ya kuma ba jam’iyyar da sauran al’ummar kasar tabbacin cewa zai ci gaba da fafutukar dora ka’idojin dimokuradiyya a cikin harkokin siyasa da kuma al’amuran da suka shafi siyasa da mulki.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce “A yau, ya kamata mu yi farin ciki da cewa jam’iyyar ta yi jinyar raunukan da ta samu, ta kuma warkar da kanta yadda ya kamata, domin tunkarar kalubalen zaben jiha-jiha da na kasa baki daya mai zuwa,” in ji shugaban.
“Idan na tuna da manufofin gwamnati kan tattalin arziki da kuma musamman ma a fannin bunkasa noma, samar da ababen more rayuwa, da kirkire-kirkire da kuma matakan jin dadin da muka sanya wa mata, matasa da marasa galihu a cikin al’umma, ina samun sabon kwarin gwiwa cewa 'yan kasarmu za su ci gaba da marawa jam'iyyar APC baya a zabenmu."
"Gwamnatinmu tana aiki don ci gaban kasa, in ji shugaban. Manufofinmu da shirye-shiryenmu ba komai suke nufi ba illa ci gaban kasa da al’ummarta.
Ku Duba Wannan Ma Shugaba Buhari Ya Ce Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC Ya Farfado Da KimartaShugaba Buhari ya sake yabawa wanda ya hada babban taro karkashin jagorancin Mai Mala Buni kan yadda aka gudanar da taron da ya kai ga kafa kwamitin zartarwa na kasa karkashin jagorancin Adamu, yana mai cewa “muna muka godiya matuka ga duk abubbuwan da ka yi ba."
Ya kuma bukaci sabon Shugaban jam’iyyar da ya kasance mai gaskiya da rikon amana kamar yadda aka san shi da shi a duk harkokinsa.