Shugaban wanda ya ke magana a zantawa ta musamman da gidan talabijin na kasa NTA, ya ce rashin hada kai ne da son zuciya ya sanya PDP ta sha kaye a zaben 2015 da hakan ya kamata a yanzu ya zama darasi ga ‘yan APC masu mulki.
Shugaba Buhari, ya ce duk mai son samun mukamin jam’iyyar a babban taron ta, ya yi kamfen don sam ba wanda za a nada haka kawai.
Da ya ke amsa tambaya kan dalilan sa na kin sa hannu kan sabuwar dokar zabe ta ba da dama a yi ‘yar tinke a zaben fidda gwanin jam’iyya, shugaban ya ce ya dau matsayar damar baiwa dukkan 'yan jam’iyyu su zabi tsarin da su ke son amfani da shi cikin 3 da su ka hada da ‘yar tinke, yin zaben ta hanyar wakilai ko sasantawa.
Kazalika, ya ce ba don zaben sa ta hanyar ‘yar tinke ya sa shi lashe zaben 2015, ya samu nasarar ce don hadin kan jam’iyyun adawa.
Ya kuma kara da cewa bai amince da tunanin shugabannin Majalisar Dokokin Najeriya ba, domin su ba ‘yan amshin shatan sa ba ne, ko a ce ‘yan amshin shatan sashen zartarwa ba ne.
Buhari ya ce shugabannin Majalisar ‘yan jam’iyyar sa ce ta APC don haka akwai fahimtar juna a tsakani don ba za su so su yi aikin da ya sabawa muradun jam’iyya ba.
ya kuma godewa shugaban Majalisar Dattawan Ahmed Lawan wanda ya ce ya zauna a Majalisar Wakilai kusan wa’adi uku kafin ya shiga Majalisar Dattawa, hakanan ya ce ya na ganin kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila tun a can baya ya na mikewa a gaban Majalisa ya na kare muradun ‘yan hamaiya.
Game da wanda zai marawa baya a zaben 2023, shugaban ya ce zai boye sunan sa a zuciyar sa don in ya baiyana za a iya hallaka shi.