Shugaba Buhari Ya Gana Da Wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC

Shugaba Mohammadu Buhari

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayi wata ganawa ta musamman da wasu gwamnonin jam’iyyar APC, inda sukayi nazari da jinjinawa shugaban dangane da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Cikin irin nasarorin kuwa sun hada da inganta sha’anin tsaro da kubutar da ‘yan matan Chibok 21 da kuma yunkurin da gwamnatin ke yi na ci gaba da samo sauran ‘yan matan, haka kuma da yadda harkar noma ke samun ingantuwa a fadin kasar.

A wata hira da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa yayi da kakakin shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu, ya tabbatar da cewa gwamnonin na jam’iyyar APC sunyi na’am da irin matakan da shugaba Buhari ke dauka wajen gudanar da Najeriya musamman a bangaren sha’anin Noma.

Game cece kucen nade naden Jakadu da shugaban kasa yayi, Mallam Garba Shehu yace tun lokacin da Buhari ya kafa gwamnatinsa akwai kyakkyawar fahimta tsakaninsa da gwamnonin jihohi, kuma akwai lokacin da ya ambaci cewar ba zai shiga sha’anin nade naden gwamnoni ba, haka kuma baya tsammanin suma zasu tsoma baki a nashi nade naden.

A yanzu dai wasu yan siyasa da aka nada a jerin sunayen Jakadun Najeriya a kasashen waje, kamar su Dakta Usman Bugaje na jihar Katsina da Pauline Tallen ta jihar Plateau sunce a kai kasuwa.

Yanzu haka ana samun bayanai kuma dake nunin cewa shugaba Buhari ya nemi wasu gwamnonin dake da korafi dangane da nade naden da akayi da su aiko da koke kokensu a rubuce domin gwamnati tayi nazari ko zata dauki matakai yin gyare gyaren da ya kamata ayi.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Ya Gana Da Wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC - 4'09"