Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kudirin Dokar Kare Bayyanai a Majalisa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci Majalisar Dattawan kasar su amince da wani kudurin dokar kare bayyanai wanda sashin zartarwar gwamnatin Najeriyan ya gabatar a Majalisar.

Kamar yadda dokar kasa ta tanadar a sashi na 58 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka yiwa kwaskwarima a shekara ta alib dari tara da casa’in da tara.

Shugaban ya bayyana wannan bukatar tasa ne cikin wata wasikar da ya aikewa Majalisar wanda aka karanta a zaman da Majalisar tayi a jiya Talata.

A cikin wasikar, shugaban yace “na gabatar da wannan kudiri na dokar kare mahimman bayyanai ta Najeriya a gaban wannan Majalisar domin tayi nazari akai kana ta tabbatar da shi a matsayin doka”

Makasudin samar da wannan doka shine domin kare hakkin ‘yancin ‘yan kasa ta yadda ya shafi bayyanan su kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Nigeria's President Muhammadu Buhari looks at a sample of the new N1,OOO note

Manufar dokar ita ce samar da tsarin dokar kariyar bayyanai mutane da kuma kafa hukumar kare bayyanai na Najeriya da zata sa ido akan dokokin bayanan jamma’an.

Daga cikin wasu mahimman abubuwan da dokar ta kunsa, akwai batun tsarin yadda za a rinka sarrafa bayyanai mutane, inganta tsarin yadda za a gudanar da bayyanan mutane ta hanyar da zata kare tsaron bayyanan nasu da kuma samar da sirranta masu bayanan da kuma tabbatar da an mu’amalanci mahhiman bayyanan da adalci, ta hanyar shari’a.

Shugaba Buhari a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya (AP)

Baya da hakan, dokar zata taimaka wajen kare bayyanan mutane da kuma samun wani abun dogaro idan an samu sabani a bangaren bayyanan mutane, tabbatar da cewa, masu kula da bayannan sun yiwa mutane adalci a game da bayyanansu.

Idan ba a manta ba, a shekara ta 2022 ne shugaba Muhammadu Buhari ya bada amincewarsa wajen kafa cibiyar kula da mahimman bayannani wanda Dr. Vincent Olatunji yake jagoranta a matsayin kwamishana domin tabbatar da an bi tsarin kare mahimman bayyanai na Najeriya.