Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Badi

Shugaba Muhammadu Buhari

Kasafin kudin badi ya kama naira triliyan N10.7 wanda shi ne kasafi mafi tsoka da aka taba yi a Najeriya, kuma shi ne kasafi na farko da shugaba Mohammadu Buhari ya lissafa kayan abinci iri 22 da yace karin kudin harajin bai shafa ba.

Shugaba Muhammadu Buhari yace an gina kasafin kudin akan dalar Amurka $57 a matsayin kudin gangar danyen man fetur, sannan Najeriya za ta hako mai ganga miliyan 2.180 na danyen man fetur kowacce rana, kana za a sayar da dalar Amurka daya akan naira N305.

Shugaban kwamitin noma a majalisar Dattawa Sanata Abdullahi Adamu, yace wannan kasafi ne da zai fitar da manoma daga cikin kangin fama da wahala, a mayar da su dangin manoman zamani masu kayan noman zamani, kuma su yi noman zamani da za su sayar kamar kowace kasa da ke da manoma irin Najeriya.

Shi kuwa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, yace ana kasafi amma bai taba ganin kasafi na gaskiya irin wannan ba, domin a wannan kasafin ne aka ce sai an gama ayyukan da ke kasa kafin a kirkiro wasu sabbi.

Daga karshe wannan kasafi a cewar shugaban kasa, ana sa ran samun kudin shiga har na naira triliyan N8.1, kuma shi ne kasafin da ake sa ran aiwatar da shi daga watan Janairu zuwa Disamba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

A saurari cikakken rahoto daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Naira Triliyan 10.7