Buhari Ya Bukaci Sabbin Ministoci Su Maida Hankali Kan Manufofi 4

Shugaba Muhammadu Buhari

Bayan ya rantsar da sabbin ministocinsa, shugaba Buhari ya ce su fi maida hanakali akan maufofin gwamnatinsa guda 4.

A lokacin da yake rantsar da sabbin ministocisa, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fada musu cewa burin gwamantinsa shine a tabbatar da manufofin ta guda hudu da ya hada da samar da tsaro, ayyukan yi, bunkasa tatalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaba Buhari ya bukaci sabbin ministocin da su yi amfani da wannan domin su tabbatar sun kamanta adalci da gaskiya wajan yin aiki ga dukkan ‘yan kasa ba wai kawai wadansu muhimman mutane za a himmatu ga yi wa aiki ba.

Sannan ya kara jawo hankalinsu da su yi amfani da wannan damar da suka samu, wajan tabbatar da cewa sun bada gudunmuwar farfado da rayuwa da kimar Najeriya da kuma ci gaban kasa.

Ministan Albarkatun Ruwan Najeriya, Injiniya Suleiman Adamu, ya ce ita gwamnati dai alkibilar ta daya ce, don haka ya kamata duka ministocin su hada kansu wajan yin aiki tare don cinmma burin shugaban kasa.

Ita ma sabuwar Ministar Ayyukan Jinkai Sadiya Umar Faruk, ta ce wannan ba wani sabon aiki ba ne, kuma za su yi iyakacin bakin kokarinsu wajan ganin ‘yan gudun hijira sun koma gidajen su.

Saurari cikakken rahoton Umar Farouk Musa daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Ya Bukaci Sabbin Ministoci Su Maida Hankali Kan Manufofi 4