Shugaba Buhari ya bayyana yadda ya ce gwamnatin sa ta mutunta matasa ta hanyar sanya hannu kan kudurin dokar karancin shekaru wajen hurumin takara.
Shugaban wanda ke jawabin murnar cikar Najeriya shekaru 58 da samun 'yanci, ya tabo muhimmanci tsaro da kara nanata cewa gwamnatin za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Nan take dan jarida Umar Gombe da ya saurari jawabin ya ce da sauran rina a kaba. Abun dake bashi takaici shi ne yadda ake wasa da abubuwan da suka shafi rayukan al’umma a kasashen Afirka musamman a Nigeria. Yayinda shugaban ke jawabi ana ci gaba da kashe kashen mutane a Zamfara da Jos amma babu wani matakin da aka dauka. Y ace kwana kwanan nan ana ta kasha kashe a hanyar Birnin Gwari amma gwamnan Kaduna ya fito ya ce ana ruruta jita jita ne.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa za ta tabbatar hukumar zabe na aiki cikin 'yanci kuma kuri'un mutane su yi aiki.
Hakanan ya nuna takaicin yadda wasu ke yada kiyayya ta amfani da yanar gizo, ya na mai cewa duk da bambance-bambance da ke tsakanin mutane, ya na da muhimmanci a hadu kan ginshikan hadin kan kasa don zama tare da girmama juna.
Isa Mu'azu Darma jami'in labarun tazarcen shugaba Buhari ne. Ya ce bayanan shugaban na da zummar hada kan 'yan Najeriya ne don nasarar zaben 2019 da zai gamsar da kowa duk da ya yi harsashen Buhari ne zai lashe zaben. Yace Buhari ya yi mulkin an gani. Abu ne a bayyane wanda duk dan Nigeria ya gani. Sai dai ba’a rasa abubuwan da ‘yan adawa ke yayatawa suna kuma gudanarwa. Bayan Buharin duk wani bincike da za’a iya yi ba za’a samu inda shugaban ya saci ko kwandalar gwamnati ba.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5