A ci gaba da ziyarar aiki da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke yi a jihar Jigawa ya bude wasu hanyoyin mota da cibiyar samar da ruwa mai amfani da hasken rana a Jihar.
Yayin da yake jawabi, gwamnan Jigawa Badaru Abubakarya ce mun gaji jimlar lita miliyan 4 da ake samarwa a Dutse yanzu, wannan cibiya zata rinka samar da karin lita miliyan 9 , idan aka tattara lita miliyan 13 kenan, amma abin da ake bukata domin wadata a Dutse da kewaye shine lita miliyan 25.
Alhaji Ibrahim Mohammed Garba Hannun Giwa dake zaman kwamishinan ruwa na Jigawa ya yi bayani kan yadda cibiyar ruwan zata rinkan aiki. A cewarsa katafaren cibiyar ruwa sabbi kashi hudu ne da suke da rijiyoyi 35. Wadda shugaban kasa ya kaddamar tana da rijiyoyi 10 kuma dukansu hasken rana ne ke sarrafasu domin a samu ruwa. Bayan shekaru biyu zasu kammala wani katafaren cibiyar ruwa da zai samar da lita miliyan 25 kowace rana
Baya cibiyar ruwa shugaban na Najeriya ya kaddamar da hanyoyi guda biyu da gwamnatin Jigawa ta gada kuma ta kammala a yankin kasar Hadejia, har ma kwamishinan ayyuka dasufuri na Jigawa Aminu Usman ke cewa, a yanzu sha’anin sufuri zai saukaka a yankin.
Yayin da jami’an gwamnatin ta Jigawa ke farin cikin shugaba Buhari ya bude wadannan aikace aikace, su kuwa ‘yan hamayya na cewa ne tsari na hankaka mai da dan wani naka. Nasiru Laraba wani dan Jam’iyyar PDP ne a Jigawa. Y ace a wasu wuraren kaman Hadeija babu wani abu sabo da gwamnatin ta yi nata na kanta. A yankin Dutse kuma sai dai aikin sola da shugaban ya bude kuma shi din ma shugaban karamar hukuma ne yake aikin.
A ranar Talatar nan ce dai shugaba Buhari ke kammala ziyarar tasa ta yini biyu a Jigawa.
Ga rahoton Mahmud Kwari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5