Shugaba Buhari Ya Bayyana Nasarori Da Gwamnatinsa Ta Samu A Fannin Tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bukin ritayar tutocin soji 53

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinta ta samu nasara ainun wajen shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin ritayar tutoci 53 da aka gudanar na rundunar sojojin kasar.

Shugaban Najeriya muhammadu Buhari ya bayyana irin dimbin kalubalen tsaro da ya taras lokacin da ya amshi mulkin Najeriya shekaru takwas da suka gabata. da suka hada da, murkushe mayakan Boko Haram, ceto wadanda mayakan su ka yi garkuwa da su da dama, da kuma shawo kai da sake tsugunar da daruruwan mayaka da su ka ajiya makamai su ka mika wuya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bukin ritayar tutocin soji 53

Da yake tsokaci kan irin yadda aka tunkari matsalar tsaron tun farko, Shugaba Buhari yace, jim kadan bayan hawansa mulki, sun sami nasarar shawo kan matsalar masu satar mutane don neman kudin fansa, yan aware, masu satar mai da sauran masu aikata manyan laifuka.

Janar Buhari yace cikin shekaru takwas da yayi yana mulki, ya bada umarnin daukar zaratan sojoji sama da dubu sittin, banda dubban hafsoshin da kowacce shekara ake yayewa daga makarantar horas da hafsoshi ta kaduna.

Dangane kuma da batun kayan aiki, Shugaba Buhari yace bayan irin hobbasan da yayi na samarwa sojojin daruruwan motocin sulke da harsasai basa iya ratsa su, da sauran kayayyakin aikin soji, an kuma sayi jiragen sama na aikin soji na zamani, tare da horas da jami'an sojin a fannin amfani da kuma kula da su.

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bukin ritayar tutocin soji 53

Ya kara da cewa, an samarwa sojojin manyan bindigogin Artillary,
bindigogi masu sarrafa kansu, da dimbin harsasai daban daban da suka yi matukar tisiri a sauya rawar da sojojin Najeriya ke takawa wajen fuskantar kalubalen tsaro.

A bayaninsa dangane da bukin ritayar tutocin, kakakin Sojin Najeriyar, Janar Nwachukwu yace ana yi wa tuta ritaya ne bayan ta dade ana aiki da ita ko ta tsufa ko kuma aka kirkiro wata sabuwar tutar runduna a barikin soji.

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bukin ritayar tutocin soji 53

Duk da dumbin nasarorin da Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta cimma a fannin, tsaro, rahotanni na nuni da cewa, ana fama da hare-haren 'yan bindiga da kuma yawan garkuwa da mutane da neman kudin fansa a sassa dabam dabam na kasar musamman a Arewacin Najeriya.

A hirar su da Muryar Amurka, wadansu 'yan gudun hijira da kuma masu kula da lamura sun bayyana matsayin tsaro a Najeriya a matsayin ci gaban mai shiga rijiya.

Rahoto na baya bayan nan da wata cibiyar bincike ta fitar na nuni da cewa, an yi garkuwa da sama da mutane 3,400 aka kuma kashe 564 a tashin hankalin da ke da alaka da garkuwa da mutane a fadin kasar.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari ya yi bayani kan matsalar tsaro