Kin Baki: Buhari Na Daukar Matakan Martani Ga Afrika Ta Kudu

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi suka da kakkausan lafazi a kan irin kiyayya da musgunawar da ake yi wa ‘yan Nigeria a kasar Africa ta kudu, wadda Najeriya ta taimaka ma ta ainun a zamanin wariyar launin fata.

Shugaban ya nuna bacin ransa ne a ganawar da ya yi da jakadan kasar Africa Ta Kudu da Ministan Harkokin Wajen Nigeria Geoffrey Onyeama a fadar gwamnati a Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ba za ta nade hannu ta ga ana cin zarafin al’ummarta ba. Za ta daukin matakin ganin an kawo karshen wannan batu da ake Allah wadai da shi a Najeriya.

Tuni shugaba Buhari ya aike da wakilinsa na musamman don ganawa da Shugaban Africa ta kudu Cyril Ramaphosa a kan kukan Najeriya da kuma neman matakan da za a dauka domin a kawo karshe wannan kashe kashen da kuma ta’adin da ake yi wa ‘yan Najeriya.

Da ya ke yi wa manema labarai bayanin bayan an kammala taron, Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya ce ana bukatar za a biya diyya kuma a tabbatar da an hada jami’an tsaron Najeriya sun yi kafada da kafada da jami’an tsaron Afrika ta Kudu domin an tabbatar da adalci dangane da wannan lalura.

Minista Onyeama ya ce ana duba yiwuwar tura jami’an tsaro daga Najeriya su je Afrika ta Kudu ta ofishin jakadancin Najeriya dake can, kana su yi aiki tare da jami’an ‘yan sandan kasar, abin da muke ganin cewa zai kasance muhimman matakai da za su kawo karshen hallaka ‘yan Najeriya a nan gaba a Afrika ta Kudu.

Ga rahoton Umar Farouk Musa daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

MARTANIN NAJERIYA GA AFRIKA TA KUDU