Tattaunawar Shugaba Tinubu Da Manema Labarai Ta Bar Baya Da Kura

Shugaba Bola Tinubu (Hoto: X/Bayo Onanuga)

Tattaunawar da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tattaunawar sa ta farko da manema labarai tun bayan da ya dare kujerar shugabancin kasar a watan Mayun 2023, ta janyo cece-kuce a tsakanin al'umman kasar.

Yayin da wasu suka bayyana gamsuwa da yadda Shugaban ya bayyana manufofinsa, wasu kuwa na ganin akwai bukatar ganin ayyukan sun fara yin tasiri a zahiri kafin su yarda da alkawuran da ya dauka.

Manema labarai da masu sharhi na siyasa sun yi nazari kan tattaunawar, suna fatan gwamnatin Tinubu za ta iya cika alkawurranta na gyaran Najeriya cikin lokaci.

Wannan tattaunawa ta zama wata dama ga ‘yan Najeriya don fahimtar shirin mulkin Shugaban, wanda a yanzu ya rage aiki da cikawa ga gwamnatin.

Tattaunawar, wadda ta gudana a cikin dakin taro na fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, ta maida hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziki, tsaro, walwalar al'umma, da manufofin gwamnatinsa na nan gaba.

Tattalin Arziki: Kalubale da Shirye-shirye: A cikin jawabansa, Shugaba Tinubu ya fara ne da batun tattalin arziki, inda ya bayyana cewa gwamnatin sa ta yi wa matsalolin tattalin arziki kwakkwaran tanadi, musamman game da farashin kayayyaki da karancin man fetur.

Ya ce, “Mun dauki matakin cire tallafin mai domin tsabtace tsarin mu. Wannan mataki mai wuya ne, amma ya zama wajibi domin inganta tattalin arzikin Najeriya.”

Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa za ta kara zuba jari a fannin makamashi da man fetur, tare da samar da tsare-tsaren da za su rage radadin da 'yan kasa ke fuskanta sakamakon cire tallafin.

Dangane da hauhawar farashin kayan abinci, Shugaban ya bayyana cewa ana aiki tare da ma'aikatar noma domin kara samar da abinci da saukaka wahalhalun da jama’a ke fuskanta.

Tsaro: Kula da Lafiyar Jama’a: A bangaren tsaro, Shugaban ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samar da sabbin tsare-tsare domin tunkarar matsalolin da suka dade suna addabar kasar.

“Mun fara inganta aikin sojoji, ‘yan sanda, da sauran hukumomin tsaro ta hanyarsamar da kayan aiki na zamani da horar da jami'ai”, a cewarsa.

Shugaban ya tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da daukar matakai na gaggawa domin magance hare-haren 'yan bindiga, masu satar mutane, da rikice-rikicen kabilanci da ke wasu sassan kasar.

Matasa, Rashin Aikin Yi, da Talauci: Shugaba Tinubu ya nuna damuwarsa kan halin da matasa ke ciki, musamman rashin aikin yi da ke ci gaba da tsananta. Ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta samar da damar dogaro da kai ta hanyar kara bunkasa sana'o'in hannu, koyar da matasa fasahar zamani, da habaka fannin kirkire-kirkire.

“Kowace kasa na samun ci gaba idan matasanta na da aikin yi. Muna shirinkaddamar da shirye-shiryen da za su tallafa wa matasa wajen samun abin yi mainagarta,” in ji Shugaba Tinubu.

Manufofin Gwamnati: Adalci da Dorewa: Shugaba Tinubu ya yi tsokaci kan manufar mulkinsa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kasance bisa tafarkin gaskiya, adalci, da ci gaba mai dorewa.

“Za mu tabbatar da cewa kowanne dan Najeriya ya samu abin da ya kamata daga gwamnati, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.”

Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da mutunta kundin tsarin mulkin kasar, tare da tabbatar da shugabanci nagari a dukkan matakai na gwamnati.

Kiraye-Kirayen Shugaban Kasa: A karshen tattaunawar, Shugaba Tinubu ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ba gwamnati hadin kai tare da hakuri kan wasu matakan da za su bukaci lokaci kafinsu fara haifar da sakamako.

Ya ce “A matsayina na Shugaban Kasa, ina da tabbacin cewa Najeriya za ta tashi tsaye idan muka hada kai. Muna bukatar goyon bayan ku domin cika alkawurran da muka dauka.”

~ Yusufuddeen A. Yusuf