Buhari Ya Ba Da Umurnin Gina Hanyoyi 36 - Sanata Gaya

Wata hanya a Jihar Adamawan Najeriya dake Arewa maso gabashin kasar

Gwamnatin Tarrayya ta ba da umurnin a ci gaba da amfani da kasafin kudin shekara 2016 har zuwa watan Mayun bana saboda a samu cikakkiyar shekara guda ana amfani da kasafin ganin cewa ranar 6 ga Watan Mayun bara ne Shugaba Buhari ya sa hannu ta zama doka.

Ministan Kudi Madam Kemi Adeosun, ce ta baiyana haka a wata takarda da ta aike wa hukumomin Gwamnati.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudi wanda aka yiwa lakabi da kasafin kudin gina kasa a gaban hadaddiyar majalisa a watan Disambar shekarar 2015, na kudi Naira Tiriliyan Shidda da Bilyan Saba’in da Bakwai da Miliyan dari Shidda da Tamanin, kwatankwacin Dalar Amurka Biliyan Talatin.

Ya zuwa yanzu dai alkaluma sun ruwaito cewar an aiwatar da kusan rabin kasafin kudin kamar yadda Sanata Danjuma Goje, shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a majalisar dattawa ya bayyana.

Rashin kyawon hanyoyi dake zama hujjar yajin aikin wasu ma’aikatan gwamnati kamar na ma’aikatar Man Fetur, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a yi su a kasafin kudin, kamar yadda shugaban kwamitin kula da hanyoyi Sanata Kabiru Gaya, ya yi karin bayanin cewa ana gab da fara gyare gyaren hanyoyi 36 da shugaban kasa ya umurci a gyara a fadin kasar.

Ko wadanne irin shirye shirye majalisar ke yi domin ganin kasafin kudin bana bai sami kura-kurai irin na bara ba?,

Sanata Yusuf Abubakar, daya daga cikin ‘ya’yan kwamitin kula da harkokin kudi a majalisar dattawa ya bayyana cewa kawo yanzu suna kan tattaunawa da sauran takwarorinsu domin tabbatar da kaucewa kura-kurai makamantan na bara.

An dauki likaci ana zargin ‘yan majalisar da mayar da hankali ga kawunansu maimakon talakawa da suka dora su bisa mulki.

Medina Dauda nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

SANATA GAYA: Shugaba Buhari Ya bada Umurnin Gina Hanyoyi 36 A Najeriya