Shugaba Barack Obama Da Sakatare-Janar Na NATO Sun Bude Taron Kolin Kungiyar

Shugaba Barack Obama na Amurka yana jawabi lokacin bude taron kolin kungiyar NATO, lahadi 20 Mayu 2012

Yayin da dubban 'yan zanga-zangar nuna kyamar yaki suka yi maci a titunan birnin Chicago domin nuna bacin ransu ga shugabannin da suka hallara a wurin taron.

Shugaba Barack Obama da sakatare janar na kungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen, sun bude taron kolin kungiyar kawancen tsaron jiya lahadi a birnin Chicago, tare da fadin cewa shugabannin duniya zasu tsara matakai na gaba da za a dauka a Afghanistan a wannan taron kwanaki biyu.

Mr. Obama ya fadawa taron cewa har yanzu akwai kalubale, kuma za a kara hasarar rayuka, amma muna da kwarin guiwar cewa muna kan turba ta kwarai, kuma abinda wannan taron kolin NATO ke nunawa shi ne duniya tana bayan dabarar da “muka tsara” in ji shi.

Sakatare janar na NATO yace ba za a yi gaggawar ficewa daga Afghanistan ba. Yace zasu bayyana kudurinsu a fili na kulla kawancen dogon lokaci da al’ummar Afghanistan har bayan janyewar sojojin kasashen waje a 2014 domin tabbatar da cewa kasar ba ta sake zamowa makwancin ‘yan ta’adda ba.

Tun fari a jiya lahadin, shugaba Hamidu karzai na Afghanistan ya jaddada kudurin gwamnatinsa na kammala karbar dukkan ayyukan tsaron kasar a shekara mai zuwa kafin a janye sojojin kasashen waje a 2014 ta yadda Afghanistan ba zata ci gaba da zamowa mai dora nauyi sosai kan kasashen duniya ba.

A halin da ake ciki, dubban masu adawa da yaki sun yi zanga-zanga a titunan birnin Chicago domin nunawa shugabannin dake halartar taron kolin NATO bacin ransu.

An dai yi zanga-zangar cikin lumana, sai ya zuwa karshe a lokacin da ‘yan sanda suka yi artabu da wasu da suka nemi tsallaka shingen da aka kafa domin hana masu zanga-zangar kaiwa ga zauren taron.